DSS Sun Titsiye Ƴan’uwan Bawa Da Wasu Ma aikatansa Tare Da Ƙwato Motaci Masu Sulke

DSS din sun kuma titsiye shugabar ma’aikatan bawa ɗin, Hadiza Gamawa, tare da mai ba shi shawara kan harkokin shari’a, U.U. Buhari.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta gayyaci wasu ƴan uwa dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, domin amsa tambayoyi.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne dai ya dakatar da Bawa daga mukaminsa tun a ranar 14 ga watan Yuni.

Tun daga wannan lokacin, Bawa na tsare a hannun DSS ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Sai dai Daily Nigerian ta tattaro cewa kwanan nan hukumar DSS ta gayyaci ƴan uwan Bawa su biyu, Yazid Bawa (wanda ke aiki a EFCC din) da Bashir Bawa (wanda ke aiki a NCC) don amsa tambayoyi.

Wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Nigerian cewa jami’an tsaron sun karɓe wata mota mai sulke (mai tare harsashi) da sabuwar mota kirar Mercedes-Benz da ake zargin daga hannun ƴan uwan ​​Bawa ɗin.

DSS din sun kuma titsiye shugabar ma’aikatan bawa ɗin, Hadiza Gamawa, tare da mai ba shi shawara kan harkokin shari’a, U.U. Buhari.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsare wadanda ake zargin ne a ranar 25 ga watan Agusta, inda bayan ƴan kwanaki sai aka sake su.

A ranar 31 ga watan Agusta, jami’an DSS din sun kuma kama mataimakan Mista Bawa, Rufa’i Zaki, da Daniela Jimoh.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *