DSS Ta Kama Manajan Jirgin Kasa Na Abuja-Kaduna A Najeriya

Kamen na shi ya biyo bayan fallasa sanarwar gargadin harin ta’addanci da za a kai kan layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama Manaja, Abuja- Kaduna Train Services, Pascal Nnorli, bisa zargin fallasa takardar gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci.

Wata majiya mai tushe daga hukumar jiragen kasa ta Najeriya NRC da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana hakan, kamar yadda rahoton jaridar The Punch ya bayyana.

Majiyar NRC ta ƙara da cewa an kama Nnorli ne tare da Manajan Ayyuka, Victor Adamu da sauran ma’aikatan.

“Shin kun san cewa sun kama manajan mu tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata – su biyun, manajan gudanarwa da Pascal? Amma sun saki ɗaya daga cikinsu.

“Victor ya fuskanci matsala saboda sun same shi a ofishin Pascal, don haka suka kama shi tare da duk ma’aikatan Pascal suka kai su ofishin DSS. Pascal har yanzu yana can.”

Majiyar NRC ta ce kama Nnorli na da nasaba da bayanan da aka fallasa.

Ya bayyana cewa hukumar ta DSS ta yi gargaɗin cewa za a iya kamawa idan har wasikar ta bazu.

An ce an mika wasiƙar mai ɗauke da gargaɗin a ofishin Pascal

Dimokuradiyya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *