Dubun Wani Mai Shago Ta Cika Bayan Da Ya Sace ‘Yar Makwabtansa Ya Boyeta A Firiji

FB IMG 1714662963726

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wani da ake zargi da sace wata yarinya ‘yar shekara 10 tare da boye ta a cikin firiji.

Alfijir Labarai ta rawaito magana da yawun rundunar, Mansir Hassan, ya tabbatar da kama wanda ake zargin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Kaduna.

Hassan ya ce a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe biyu na rana, mahaifiyar yarinyar da aka sace, Uwaila Idris da ke kauyen Unguwar Gara a karamar hukumar Kauru ta jihar, ta kai rahoton bacewar diyarta ofishin ‘Yan sanda.

“Ta zo ofishin ‘yan sanda ne ta ba da rahoton cewa tana zargin a ranar 26 ga Afrilu, da misalin karfe daya na rana, wani Aminu Garba ya sace ‘yarta ‘yar shekara 10 mai suna Hanifa Garba a cikin shagonsa. Bayan taje aika kuma mutane sun ga shigar ta Shagon amma ba’a ga ta fito ba.

Hassan ya ce da aka tambayi wanda ake zargin game da inda Hanifa take, ya musanta cewa bai san inda take ba.

Daga nan sai ya koma shagonsa ya rufe bakinta da hijabinta sannan ya boye ta cikin Firijin sa ya kuma saka kwado ya kulle.

Sai dai Matasan unguwa da suke da tabbacin cewa tana cikin Shagon.

suka ce lallai sai an binciki shagon sa kaf kafin a yarda cewa ba shi ya sace yarinyar ba kamar yadda ya ke ta cewa, Da aka balle Shagon da karfi sai aka tarar da ita cikin firijin sai aka ga Hanifa ciki kwance.

Zuwa yanzu dai an cafke shi yana tsare wajen ‘Yan sanda a na ci gaba da bincike..

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

One Reply to “Dubun Wani Mai Shago Ta Cika Bayan Da Ya Sace ‘Yar Makwabtansa Ya Boyeta A Firiji”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *