Hukumar EFCC ta Bankado Wani Gwamna a Arewa da ya kwashi Naira biliyan 60
Best Seller Channel
Hukumar EFCC ta bayyana haka ne a sakon da take aike wa manema labarai na wata-wata mai taken EFCC Alert.
BBC ta rawaito, Abdulrasheed Bawa yana yin karin bayani game da batun a wata tattaunawarsa da mujallar da hukumar take wallafawa, ta ce gwamnan da aka gano na wata jiha ce da ke Arewa ta Tsakiya ko da yake bai fadi sunansa ba.
Zan iya gaya muku cewa sabon sashen da muka bude kan leken asiri yana aiki tukuru a fadin kasar nan.
Sashin ya bankado abubuwa da dama. Daya daga cikinsu shi ne wani gwamna a wata jiha ta Arewa ta Tsakiya, inda suka gano cewa cikin shekara shida da suka gabata (mutum daya) ya cire tsabar kudin da suka kai N60 bn.”
Best Seller Channel
“Muna kallon abubuwan da yake yi, kuma ina tabbatar muku cewa bayan mun kammala bincike, za mu sanar da ‘yan Najeriya kan abubuwan da muka yi a bayan fage game da laifukan da ake aikatawa ta amfani da shafukan intanet.
Sakon da shugaban Hukumar EFCC Kenan Bawa.