An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a kotun koli na Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, Abuja, ta hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Alfijir Labarai ta rawaito Bello, wanda rahotanni suka bayyana cewa yana boye tun watan Afrilu 2024, an kawo shi hedikwatar hukumar yaki da cin hanci ta EFCC a Abuja a ranar Talata da misalin karfe 12:55 na rana.
Daily Trust ta ruwaito cewa EFCC ta ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema bayan ya gaza amsa gayyatar da aka yi masa sau da dama, har ta kai ga an fara shari’arsa ba tare da ya halarta ba.
Jami’an hukumar sun bayyana wa jaridar a wata hira cewa an kama Bello ta hanyar dabarar bincike, sabanin rahotannin da wasu ke yadawa cewa ya je kansa zuwa EFCC.






Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj