EFCC ta kama ƴan damfarar yanar-gizo Guda 21 a Bauchi

FB IMG 1742236161930

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, shiyyar Gombe sun kama wasu mutane 21 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a ranar Asabar a garin Bauchi, jihar Bauchi.

An kama wadanda ake zargin ne bisa samun sahihan bayanan sirri kan zarginsu da damfara ta yanar gizo a yankin Kaure GRA, Bauchi da Awala, hanyar Maiduguri a jihar Bauchi.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu a wajen kama su sun hada da mota kirar BMW guda daya da Toyota Camry, na’urar wasan ƙwallon ƙafa guda 5, na’ura mai ƙwaƙwalwa masu tsada 30, talabijin guda daya, POS, injina, ipad hudu, da kwamfutar tafi-da-gidanka guda biyar.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *