EFCC ta Kama Hadi Sirika bisa zargin almubazzaranci da sama da Naira Biliyan 8

FB IMG 1713891265745

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan wani bincike da ake yi kan badakalar kudaden da suka kai N8,069,176,864.00.

Alfijir Labarai ta rawaito Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama wanda ake zargi ya bayyana a ofishin Hukumar EFCC na Babban Birnin Tarayya da misalin karfe 1:00 na ranar Talata.

A lokacin da Sirika ya isa ofishin hukumar EFCC FCT, a halin yanzu yana fuskantar tambayoyi daga masu binciken EFCC game da badakalar bada kwangilar da ya ba wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited, mallakin kanin sa Abubakar Sirika.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *