Labari Mai Dadi! Majalisar Wakilai Ta Amince Da ‘Yancin Kananan hukumomi Tare Da Mai Da Zabensu Hannun INEC Ta Kasa

IMG 20230923 WA0013

Daga Aminu Bala Madobi

Gyaran dokar da majalisun suka aiwatar na cikin kudurorin da majalisar wakilai ta amince da su a makon da ya gabata, majalisar dattawa ta amince da shi a wannan rana.

Alfijir Labarai rawaito bayan jalla-kujalle da kai ruwa rana game da batun baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kan su, a yanzu haka majalisar ta amince  a baiwa kananan hukumomi yanci ta hanyar  gabatar da tasarrafin kudaden da doka ta bada damar a basu.

A wannan rana ta talata ce, majalisun dokokin kasar nan suka amince da dokar data bada dama ga kananan hukumomi kasar nan 774 damar cin gashin kansu ta hanyar kashe kudaden su.

Wannan mataki da majalisun suka dauka, ya gabata ne bayan da akayi gyaran fuska a sashi na 124 na kundin tsarin mulkin kasar nan.

Sashin na 124 dai ya fayyace dokar samar da kananan hukumomin a matsayin daya daga cikin murahun zartarwa wato tarayya da jihohi, sai kuma su kansu kananan hukumomin, ta hanyar suyi abinda suka ga dama da kudaden su ba tare da yin katsalandan daga bangaren gwamnatocin jihohin su ba.

Kwamitocin zaurukan majalisun biyu sun hada gyararrakin da suka aiwatar kan dokar wadda suka fara tun a watan maris da ya gabata.

Da wannan ci gaba, yanzu a iya cewa majalisun sun amince da dukkan sadarori 23 da kuma sashin da suka yi gyaran akai.

Rahotanni sunce za’a aike da sabon kudurin dokar ga zaurukan majalisun dokoki na jihohi domin amincewar su.

Hakazalika zasu amince da dokar samar da mai binciken kudi na kananan hukumomi, sai kuma sabuwar hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi ta jihohi.

A gefe guda kuma majalisar ta amince da kwace damar da hukumomin zabe masu zaman kansu na jihohi ke da su na gudanar da zaben kananan hukumomi, a maimakon hakan, dokar ta mika ragamar hakan ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.

A bangaren zaben dai, majalisun sun aiwatar da gyara a sashi na 65 da 106 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, inda ta amince da samar da wani bangaren da zai bada dama ga dan takara mai zaman kansa wato indifenda wanda baya karkashin kowacce jam’iyya tare da baiwa irin wadannan yan takar damar tsayawa takara a zabuka masu zuwa.

Kan wannan cigaba masana kan alamuran yau da kullum na kallon wannan gyaran fuska kan tasarrafin kudaden ga kananan hukumomi ka iya sauya cigaban yankuna wanda abaya ake zargin gwamnoni da kawo tasgaro wajan wannan yunkuri.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

One Reply to “Labari Mai Dadi! Majalisar Wakilai Ta Amince Da ‘Yancin Kananan hukumomi Tare Da Mai Da Zabensu Hannun INEC Ta Kasa”

  1. I agree with this medium of information, because they are legit in terms of providing information

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *