El-Rufai Ya Hakura Da Zama Minista Ya Mika Sunan Wanda Zai Maye Gurbinsa

Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya janye sha’awar sa na kasancewa cikin majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu.

Alfijir Labarai ta rawaito majiyoyin daga fadar shugaban kasa sun bayyana mana cewa El-Rufai ya shaidawa Tinubu a wani ganawa da suka yi a ranar Talata cewa ba ya sha’awar zama minista, amma zai ci gaba da ba da gudummawar sa domin ci gaban Najeriya a matsayinsa na dan kasa.

“Ya kuma shaida wa Tinubu cewa yana bukatar lokaci don mayar da hankali kan kan Karatunsa na samun digirin digir gir a wata jami’a a kasar Netherlands.”

Majiya ya shaida wa Yan Jarida cewa tsohon gwamnan ya ba da shawarar a nada wani makusancin sa minista, mai suna Jafaru Ibrahim Sani, yana mai cewa shugaban kasa zai same shi mutum nagartacce wanda za a yi tafiyar arziki da shi.

Sani ya taba zama kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kaduna (ilimi da muhalli na kananan hukumomi) yayin da El-Rufai ke gwamna.

Tun bayan ya dawo Najeriya daga Landan, El-Rufai ya nemi ganawa da shugaban kasa, a wannan lokaci ya samu labarin kin tabbatar da shi da majalisar dattawa ta yi.

A ganawar, shugaban kasa Tinubu ya sanar da El-Rufai cewa ya samu korafe korafe akan sa masu yawan gaske, da yana bukatar rana daya domin ya duba su da kyau sannan ya san wani mataki zai dauka.

A daidai wannan lokaci ne El-Rufai ya shaida wa Tinubu cewa, ya hakura da kujerar ministan, tunda karara na ji a jikina akwai wasu zagaye da shugaban Kasa da basu so na zama minista.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *