Engr Rabiu Kwankwaso Ya Magantu Akan Kungiyar Kano Pillars

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa kwankwaso ya taya kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars murnar komawa gasar Firimiyar Najeriya.

Alfijir Labarai ta rawaito sanata Rabi’u Musa kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan wasa da hukumar gudanarwar kungiyar a gidansa da ke gundumar Maitama a Abuja da yammacin yau (Asabar).

Ya yaba musu bisa wannan aikin da suka yi da kuma yi musu fatan samun nasara a gasar Firimiyar Najeriya ta 2023/2024 mai zuwa.

Tun da farko Shugaban kungiyar Alhaji Babangida Umar Little Said ya ce, sun je gidansa ne domin gabatar masa da kofin zakarun na biyu da suka lashe a gasar Super 8 ta Najeriya da aka kammala na shekarar 2023 tare da neman saka albarkar ci gaban kungiyar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *