Hukumar NSCDC Ta Baje Kolin Mutun 27 Kan Zargin Aikata Manyan Laifuka

Shu’aibu Ibrahim Gusau

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, Sani Mustapha, ya Baje Kolin wasu mutane 27 da ake zargi da Aikata satar wayoyin hannu, (salula) da hada Kai da kungiyar barayi.

Alfijir Labarai ta rawaito da yake gabatar da wadanda ake zargin a shalkwatar hukumar (NSCDC) ta jihar da ke Gusau, Sani Mustapha ya ce wasu mutane 27 da ake zargi wadanda ke cikin wasu kungiyoyin masu aikata laifuka da suka ƙware wajen satar waya da sauran miyagun ayyuka.

Ya kara da cewa, jami’an hukumar ne suka kama su a lokacin da suke sintiri a garin Gusau musamman a Unguwar Tudun Wada da sauran wurare masu hadari .

Kwamandan ya ce, an kama wadanda ake zargin da muggan makamai kamar su wukake da igiyoyi da ake amfani wajan shake mutane.

Hakama ya kara da cewa sun kama wasu ‘yan mata uku ‘yan kasa da shekara 20 da misalin karfe 23:30 na dare tare da wasu abubuwa da ake zargin na sa maye ne a kusa da Top Town Hotel da ke Gusau. Kwamandan ya tabbatar wa jama’a cewa ya kammala shirye shiryensa na gurfanar da barayin gaban kuliya.

Ya ce, an kuma kama daya daga cikin wadanda ake zargin sanye da kakin soji a hannunsa wanda yake amfani da shi wajen muzgunawa wadanda abin ya shafa.

Inda ya kara da cewa, an kama kayan da ake amfani dasu wajen hada takin zamani har buhu 108 a hannun wasu haramtattun dillalan kayayyakin, don haka ya ce za a gurfanar da duk masu hannu a cikin wannan haramtacciyar fatauci a gaban Kotu .

Sai dai kwamandan ya gargadi ‘yan ta’adda da ‘yan iska da su kaurace wa jihar domin rundunar tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro a shirye suke domin kawar da duk wani nau’in ta’addanci a jihar.

Sai dai ya shawarci jama’a da su yi taka tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani motsi da ake ganin yana iya zama barazana ga harkar tsaro, hukumar da tsaron domin daukar matakin da ya dace

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *