Falalar Ramadan! Gwamna Ya Bawa Ma’aikatan Jihar Rabin Albashinsu Kyauta

IMG 20240311 WA0047

Muna matukar son ganin farin Ciki da walwala a fuskokin al’ummar jaharmu Mai albarka.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya bawa ma’aikatan jihar rabin albashinsu don kyautata musu albarkar watan Ramadhan

Saboda Martaba da girma na watan Azumin Ramadan tare da kuma tausayawa da kulawa ga ma’aikata jihar Sakkwato, gwamnan ya bayar da damar a biya wani sashe daga cikin Albashin kowane ma’aikachi daga jiya lahadi domin saukakawa ga al’amurran yau da kullum a cikin Azumi.

A Jawabin Gwamnan da Yayi kan batun biyan kudin ga ma’aikata jihar ya ce “muna matukar son ganin farin ciki a fuskokin al’ummar jahar sokoto” Wannan abin alherin da gwamnan ya yi wa ma’aikatan jihar da ma ‘yan kasuwa suna ta yabawa da fatan alheri gareshi.

kamar yadda Mai magana da yawun Gwamnan Abubakar Bawa ya shaida wa Jaridar Alfijir Labarai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *