Fallasa! Takardun kotu sun baiyana yadda Ganduje ya sayar da kamfanin sarrafa auduga ga ƴaƴansa

IMG 20240202 194808

Wasu takardun kotu sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayar da wani kamfanin sarrafa auduga mallakin jihar Kano, dake unguwar Challawa Industrial Ltd, ga wani kamfani mai suna Lesage General Enterprise Ltd.

Alfijir labarai ta rawaito a makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Kano ta maka Ganduje, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa a kotu tare da matarsa ​​da dansa da wasu mutane biyar bisa zargin cin hanci, da hada baki, da cin amana da sauran su.

Daily Nigerian ta wallafa cewa kamar yadda takardar tuhumar da kuma wasu shaidu da wakilin jaridar ya gani, ana zargin Ganduje da sayar da kadarar gwamnati da darajarta ta kai Naira miliyan 750, amma aka sayar da ita kan rangwamen kudi Naira miliyan 320.

Takardun sun nuna cewa ba a saka kuɗaɗen a asusun gwamnatin jihar Kano ba, yayin da aka kuma kwashe takardun mallakar kadarar daga ofishin gwamnatin jihar Kano.

Wasu daga cikin shaidun da aka gabatar a gaban kotu sun nuna cewa uwargidan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Hafsatu Abdullahi Ganduje ita ce kadai ta rattaba hannu a madadin kamfanin da ake zargi, yayin da wasu takardu suka nuna cewa ‘ya’yan Ganduje duka suna da hannun jari kuma daraktoci ne a kamfanin da akai amfani da shi wajen karkatar da dukiyar al’umma.

Kamfanin wanda ke da RC No. 115922 da adireshin sa ke lamba 201 Zoo Road, Kano, yana da Umar Asiya Abdullahi, Umar Abdulazeez Umar, Umar Muhammad Abdullahi, Zainab Abdullahi a matsayin daraktoci, yayin da Fatima Abdullahi a matsayin sakatariyar kamfanin.

Gwamnatin jihar Kano ta yi ikirarin cewa matakin na Ganduje ya saba wa tanadin sashe na 311 da aka karanta tare da sashe na 79, da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 315 na kundin laifuffuka (kamar yadda aka gyara).

Da aka tuntubi mai magana da yawun Ganduje, Edwin Olofu, ya ki cewa komai, yana mai cewa tunda maganar tana gaban kotu, kotu ce za ta tantance gaskiyar lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *