A watan da ya gabata ne dai kwamitin kwararrun ma’aikata na shari’a (LPPC) ya tantance sunan Ms Daudu tare da wasu lauyoyi 68 da za su yi takarar mukamin SAN mai daraja.
Alfijir Labarai ta rawaito Farfesa Benedicta Daudu, masaniya ce a fannin shari’a, an kama tana yin magudin jarrabawa a Jami’ar Jos (UNIJOS) wanda daga baya jami’ar ta dakatar da ita, ta kasa shiga jerin sunayen wadanda suka samu lambar yabo ta Senior Advocate of Nigeria (SAN) a shekarar 2023.
Kwamitin kwararrun Lauyoyi na (LPPC), a watan da ya gabata, ta takaita sunan Ms Daudu tare da wasu lauyoyi 68 masu daraja ta SAN.
‘Yan Najeriya da dama sun soki jerin sunayen saboda bayyanar sunan Ms Daudu a ciki.
Sai dai, sunan Ms Daudu ya bace a cikin jerin sunayen mutane 58 na SAN a jerin sunayen karshe da aka fitar ranar Alhamis.
Ba a iya sanin ko gazawar Daudu na shiga jerin sunayen yana da nasaba da matsalar jarrabawar da ta samu a baya.
Da yake sanar da sakamakon karshe na zaben a ranar Alhamis, LPPC karkashin jagorancin alkalin alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola, ya ce, an yi watsi da dukkan korafe-korafe hudu da aka samu na rashin cancantar wadanda aka zaba.
“Taron ya kuma yi la’akari da koke-koke daban-daban guda hudu (4) da aka rubuta a kan wasu daga cikin wadanda suka gabatar da bukatar, kuma sun tabbatar da cewa kowace korafe-korafen ba shi da wani abin da ya dace, aka yi watsi da su.
Sai dai kwamitin bai bayyana ko Ms Daudu na daya daga cikin wadanda suka shigar da kara suka kalubalanci cancantar su ba.
Ba a kuma bayyana sunan duk wanda aka kalubalanci cancantarsa ba a cikin koken.
An keɓe wannan matsayi ne ga lauyoyin Najeriya waɗanda suka bambanta kansu a fannin shari’a, ko dai a fagen bayar da shawarwari ko kuma a fagen ilimi.
Hakanan mutunci da martabar ‘yan takarar na daga cikin manyan abubuwan da ake la’akari da su kan kyautar.
Premium Times ta bayar da rahoto sosai kan yadda mahukuntan Jami’ar Jos (UNIJOS) ta Jihar Filato suka dakatar da Malama Daudu daga zaman karatu daya bayan da aka kama ta tana “magudi” a jarrabawar kammala karatun digiri a shekarar 2016.
Ms Daudu, wadda a lokacin tsohuwar farfesa ce a fannin shari’a, kuma shugabar Sashen Shari’a da Dokokin kasa ta tsangayar shari’a a UNIJOS, an kama ta da laifin zamba, yayin da take jarrabawar digiri na biyu a fannin bincike da manufofin jama’a a tsangayar ilimin zamantakewa jami’a.
Sashen bincike da manufofin jama’a na UNIJOS ya zarge ta da yin fasa-kwaurin amsoshi da aka shirya a lokacin jarrabawar Global Context in Public Policy.
Majiyoyi sun ce daga baya an kai rahoton lamarin ga kwamitin jarrabawar jami’ar, amma wasu dalibai da malaman jami’o’in sun yi ikirarin cewa an yi yunkurin rufa-rufa da hukumomin jami’ar.
Kokarin da mahukuntan jami’ar suka yi na hukunta Ms Daudu bisa matsayinta na malamar karatu ya ci tura saboda wani matakin shari’a da ta dauka a kan jami’ar.
Sai dai jami’ar a watan Disambar 2016, ta dakatar da ita yayin da take kokarin gudanar da bincike kan lamarin.
Amma daga baya an samu labarin cewa Ms Daudu da hukumar ta UNIJOS sun cimma matsaya, inda ta yi murabus daga nadin nata aka biya ta.
Daga nan ne ta tafi Jami’ar Jihar Taraba, inda ta zama Farfesa a shekarar 2019.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo