Alfijir Labarai ta rawaito Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdulahi Umar Ganduje, ya bukaci Babbar Kotun Jihar da ta hana Hukumar EFCC ci gaba da bincikensa kan bidiyon Dala.
A shekara ta 2018 ce dai wata jaridar intanet mai suna Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayan bidiyo indas a cikinsu ake zargin Ganduje da karbar cin hanci da Dalar Amurka, daga hannun wasu ’yan kwangila.
To sai dai a kwafin wata kara da Gandujen ya shigar, wacce Aminiya ta yi tozali da ita, ya nemi kotun da ta bayyana cewa bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki, haramun ne EFCC ta binciki lamarin wanda tuni yake gaban Majalisar Dokokin Jihar.
An dai shigar da karar ne ranar 23 ga watan Maris, ’yan kwanaki kafin tsohon Gwamnan ya mika ragamar mulkin jihar.
Kazalika, bincike ya nuna an kai wa EFCC takardun kotun ne ranar 5 ga watan Maris.
Lauyoyin da suka shigar da karar a madadin Babban Lauyan Jihar sun tabbatar mana da cewa har yanzu karar tana gaban kotun, amma sun yi alkawarin bincikawa su yi mana karin bayani kafin zama na gaba.
Masu karar sun kuma bukaci kotun ta bayar da umarnin da zai hana “wadanda ake karar ko jami’anta ko ’yan korarta ko wasu da za ta fake da su ko ta wacce fuska daga ci gaba da gayyata, bincika, yin titsiye ko kuma daukar kowanne irin mataki ta kowacce fuska da ke da alaka da bidiyon Dala a kan Ganduje har sai Majalisa ta kammala nata binciken.”

Idan za a iya tunawa, Ganduje tun a lokacin ya sha karyata sahihancin bidiyoyin, inda ya ce kagaggu ne.
Daga bisani dai Majalisar ta kafa kwamitin a lokacin, kodayake har zuwa karshenta ba ta bayyana wa jama’a sakamakon binciken nata ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Wani Aikin sai qasata Nigeria Barayi Sune suke bincikar mutane sunyi sata
Ga dai Bawa Nan An damqe shi bisa zargin sama da Fadi