Alfijir Labarai ta rawaito tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ko a jikinsa, game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na ci gaba da binciken bidiyon dala, wanda ake zargin an nuna shi yana karbar cin hanci da rashawa.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Muhuyi Magaji Rimin Gado ya koma kan kujerarsa, bayan da tsohuwar gwamnatin ta tube shi, ya bayyana dawo da binciken da aka fara tun lokacin da bidiyon ya bulla.
Magaji ya ce baya ga bidiyon dala ma, akwai wasu zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin ta Ganduje da ta gabata na yin wadaka da baitulmalin jihar musamman kudaden kananan hukumomi, da maganar kwangiloli da kudaden haraji.
Sai dai tsohon kwamishinan watsa labaran jihar Muhammad Garba, wanda na hannun daman tsohon gwamnan Kanon Abdullahi Ganduje ne, ya ce wannan abu ba ya daga masu hankali ko kadan.
A cewar Malam Muhammadu Garba ”Magana ce ta kotu, kuma shi Muhuyi a matsayinsa na lauya ya fi kowa sanin me ya kamata ya yi, mun zuba ido mu ga abun da za su yi, idan yana da dama ya binciki maganar da ke kotu ya fi kowa sani, idan ma ba shi da dama ya fi kowa sani”.
Ya kara da cewa ”ko da na yi magana da Ganduje abun bai dame shi ba, saboda haka wannan lamari ne na shari’a.
Garba ya ce idan ta kama tsohon gwamnan ya je idan an gayyace shi zai nemi shawarar lauyoyi kan abun da ya kamata ya yi.
A baya-bayan nan ne dai tsohon gwamnan Ganduje ya nemi kotu, ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC daga duk wani bincike a kan lamarin bidiyon dalar, bisa hujjar cewa hukumar ba ta da damar gudanar da bincike kan lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐲𝐚𝐧 𝐛𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐦𝐮𝐡𝐮𝐲𝐢 𝐝𝐚 𝐲𝐚𝐛𝐢𝐧𝐤𝐢𝐜𝐢 𝐠𝐰𝐚𝐦𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐧𝐝𝐮𝐣𝐞,𝐀𝐤𝐚𝐧 𝐟𝐞𝐟𝐚𝐧 𝐝𝐚𝐥𝐚
Bincike tabbas sai anyi domin a maidowa kanawa kimar su, Gandola ake ce mana yanzu a kudan cin kasar nan. Ina dalili , da mutuncin mu.
Wake daya inji bahaushe shi kan bata gari.