Kungiyar Kwadago Ta Gargadi Gwamnatin Tarayya Kan Kudin Wuta

Alfijir Labarai ta rawaito Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na yin ƙarin kuɗin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 cikin wata mai zuwa.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya fitar, ya ce matakin zai ƙara wa ‘yan ƙasar musamman talakawa ”wahalhalu da matsin da suke ciki”.

Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasar NERC na shirin ƙara kuɗin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

A wani mataki na janye tallafin da gwamnatin ƙasar ke biya kan kudin wutar lantarkin.

BBC ta tuntuɓi hukumar ta NERC, don jin bahasinta kan matakin, to amma jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Michael Faloseyi ya ce ba a ba shi izinin yin magana kan batun ba.

‘Yan ƙasar da dama sun bayyana kaɗuwarsu kan matakin ƙarin kuɗin wutar lantarkin, suna masu fargabar cewar zai haifar musu da ƙarin matsin tatalin arziki.

A watan da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da matakin janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man fetur da na kayan abinci a faɗin ƙasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *