Ganduje Ya Turawa Atiku Da Peter Obi Sako Kan Tabbatar Da Tinubu A Shugaban Ƙasa

FB IMG 1695973222058

Ganduje ya kuma shawarci dan takarar PDP a zaben, Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi, da su yi hakuri su jira sai 2031, lokacin da Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce hukuncin Kotun Koli na tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin halastaccen zababben Shugaban Najeriya ’yar manuniya ce cewa zaben ranar 25 ga watan Fabrairu sahihi ne.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Alhamis, Ganduje ya kuma shawarci dan takarar PDP a zaben, Atiku Abubakar da takwaransa na LP, Peter Obi, da su yi hakuri su jira sai 2031, lokacin da Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu.

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya kuma taya Shugaba Tinubu murnar yin nasarar, inda ya ce hukuncin ya kawo karshen dukkan wata takaddamar tafka magudi da ’yan adawa ke zargin an yi a zaben.

Ganduje ya kuma ce hukuncin zai ba Tinubu damar mayar da hankali wajen farfado da manufarsa ta farfado da Najeriya wacce jam’iyyarsu ta sa a gaba.

Daga nan sai ya bukaci ’yan takarar da su mayar da wukarsu cikin kube sannan su hada gwiwa da gwamnatin Tinubu wajen kai Najeriya tudun mun tsira.

Shugaban na APC ya kuma roki ’yan Najeriya ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba da su ci gaba da mara wa Tinubu baya har ya kai ga cim ma kudurorinsa na alheri ga kasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *