Muna yin Allah wadai da kakkausar murya kan cin zarafin da aka yi wa ɗan jarida Abdulbaki Ali Ahmed Sharifai da ake zargin wani jami’in gwamnatin Jihar Kano, Auwal Sani Rogo (SSR), ya aikata a yayin wani taro na gasar kamun kifi ta Argungu.
Wannan abu ba wai cin mutuncin mutum ɗaya ba ne kawai — hari ne kai tsaye ga ’yancin aikin jarida, ’yancin faɗin albarkacin baki, da dimokuraɗiyya baki ɗaya.
Abin takaici, lamarin ya faru a gaban manyan jami’an gwamnati, amma har yanzu babu wata hukunci ko neman afuwa daga wanda ake zargi ko gwamnatin Jihar Kano.
Wannan shiru yana nuna rashin mutunta dokoki da kuma ƙoƙarin danne ’yan jarida.
Muna ba gwamnatin Jihar Kano wa’adin sa’o’i 24 kacal ta dauki matakin ladabtarwa kan wanda ake zargi da ya bayar da hakuri a hukumance ga ɗan jaridar
Tabbatar da kariya ga ’yan jarida a jihar
Idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za mu garzaya kotu domin neman cikakken hakkinsa tare da ɗaukar dukkan matakan doka da suka dace.
Muna kira ga kwamashinan Yan sanda jahar Kano da Yakama ya gudanar da bincike sannan a gabatar da shi a gaban kutu munada majiya mai ƙarfi kan an shigar da kurafi gaban kwamashina Yansanda jahar Kano amma yaki zuwa gaiyata da aka yi masa saboda karan tsaye akan doka
Wannan ba shi ne karo na farko ba.
Kwanan nan ma an samu cin zarafin ɗan jarida Aminu Halilu Tudunwada. Wannan yana nuna cewa cin zarafin ’yan jarida a Jihar Kano yana ƙara kamari, abin da ba za mu lamunta ba.
Muna kira ga: Kungiyoyin kare hakkin dan Adam
Kungiyoyin ’yan jarida
Lauyoyi da masu rajin dimokuraɗiyya
Al’umma baki ɗaya
da su tashi tsaye domin kare martabar aikin jarida kafin a mayar da shi abin tsoro.
’Yancin Jarida ba laifi ba ne — ginshiƙi ne na adalci da gaskiya.
✍️ Duk wanda ya ci zarafin ɗan jarida, ya ci zarafin al’umma ne baki ɗaya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t