Gobara Ta Ƙone Ofishin ‘Yan Sanda A Kano

IMG 20240212 131736

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce gobara ta kone ofishin ‘yan sanda reshen karamar hukumar Nasarawa.

Alfijir labarai ta rawaito Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano ranar Litinin cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin.

‘’Da misalin karfe 05.45 na safe ofishin ‘yan sanda ya kama da gobara ya kone wani bangare na ginin ofishin.

”Wannan ya faru duk da irin gaggawar daukar matakai da Hukumar kashe gobara ta jihar ta dauka,” cewarsa.

Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

‘’An killace yankin don hana masu shiga kallo da bata-gari shiga wurin, makamai da alburusai da ke ofishin suna suna nan a killace.

“A yanzu haka jami’in ‘yan sandan na tantance wasu takardu da abin ya shafa,” inji Kwamishina.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *