Gamnan jihar Kano Abba Kabir ya cika alkawarin daya dauka na tura yarinya Nana kasar India domin ayi mata aikin Ido.
Alfijir Labarai ta rawaito Nana ita da mahaifanta sun ziyarci mai girma gwamna a yau a gidan Gwamnatin jihar Kano, inda gwamnan yayi musu rakiya zuwa mota domin tafiya kasar India.

Idan za’a iya tunawa Nana itace yarinyar data ringa kuka a shekarar 2019 kan tana bukar ganin Abba Gida Gida.
Bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan kano, Abba Kabir ya ziyarci Gidan su Nana domin dubata da kuma gaishe da iyayenta, wanda a wannan lokacin ya fahimci yarinyar tana fama da matsala Ido a nan take Abba ya dauki alkawarin daukar nauyin ta zuwa kasar waje domin duba lafiyar idon nata wanda kuma a yau 21 /9/2023 ya cika wannan alkawarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
Allah sarki Abba jidajida Allahu ya Bata lpy ya dawo dasu lpy