Gwamna APC Ya Kamu Da Rashin Lafiya Mai Tsanani – In Ji Abdullahi Adamu

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa rashin lafiyar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta yi tsanani, yayin da ya ke fama da jiyya a kasar waje.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Jam’iyya na kasa Abdullahi Adamu ya bayyana hakan ne yayin wani taro tsakanin shugabancin jam’iyyar na kasa da shugabannin jam’iyyar ta APC na jiha suka yi a Abuja a jiya Litinin.

“Cikin alhini, ina mai sanar da ku cewar gwamnan jihar Ondo na fama da jiyya a kasar waje,” in ji Mista Adamu.

“Muna yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa,” in ji shi.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *