Gwamna Baba Zulum ya sauke Kwamishinoninsa a jihar Borno nan take

FB IMG 1774871641998

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da rushe Majalisar Zartarwar Jihar, tare da sallamar dukkan kwamishinonin sa nan take.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Bukar Tijjani, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin samar da dama ga duk wani memba na majalisar da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓukan gama gari masu zuwa.

Gwamnan ya kuma umarci dukkan kwamishinonin da abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukan ma’aikatunsu ga manyan sakatarorin ma’aikatun (Permanent Secretaries) kafin ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, 2026.

Zulum ya nuna matuƙar godiyarsa ga tsoffin kwamishinonin bisa ƙoƙari, jajircewa da gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da kuma yi wa al’ummar Borno hidima.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *