Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce za a buga sunayen wadanda suka ci gajiyar filayen da aka raba a harabar kwalejin Kano da ake ta cece-kuce akan gine-ginen da ake shirin rugujewa.
Yusuf ya bayyana hakan ne a dakin taro na African House da ke gidan gwamnatin jihar ranar Lahadi.
Matakin na janyo ce-ce-ku-ce kamar yadda akasarin masu gine-gine a filayen suka ce sun samu takardar shaidar zama da kuma amincewar gine-gine daga gwamnati.
Tuni dai suka aike da jakadu zuwa ga gwamnan da kada ya rusa kadarorin su na biliyoyin naira a cewarsu a wani taron manema labarai a ranar Asabar.
Gwamnan ya yi zargin cewa sama da kashi 70 cikin 100 na filayen an raba wa uwargidan tsohon gwamnan jihar, Dakta Hafsat Ganduje da ‘ya’yansa.
‘’Wannan wurin na talakawa ne. Maimakon gina dakunan kwanan dalibai, gidajen wasan kwaikwayo, na wasanni don amfanin ɗalibai, maimakon haka sun canza filayen don amfanin kansu, ” in ji Gwamna Abba Yusuf.
“Zan iya tabbatar muku da cewa za mu sanya shi yadda yake da kuma amfanin jama’a.”
“Akwai wasu mutane da ke ta hayaniya kan yunkurin ruguza gine-ginen da aka haramta a wurin, amma abin mamaki shi ne yawancin sun kasance cikin wadanda suka ci gajiyar rabon filayen.

Za mu buga dukkan sunayensu domin mutane su fahimci abin da ke faruwa.’’
Gwamnan ya ce an raba filayen makarantu da dama ne don amfanin kashin kansu da kuma wasu fa’idoji.
Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa abin takaici ne yadda Gwamna Ganduje ya sha rantsuwar kama aiki da kuma yin biyayya ga hakkin al’ummar da yake mulka amma abin bakin ciki shi ne ya kasance mai fafutukar kwato ‘yancin jama’a domin amfanin kansa.
Ya yi nuni da cewa, yayin da ya kuma sha alwashin kare hakkin jama’a a matsayinsa na gwamnan jihar, ba zai bari zaluncin da ake yi wa jama’a ya tafi ba tare da gyara ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ