Gwamna Ya Dakatar Da Shugaban Ma’aikata Da Dukkan Permanent Secretary

Gwamna Alex Otti na Abia ya dakatar da shugaban ma’aikata na jihar (HoS), Mista Onyii Wama, da dukkan sakatarorin dindindin na jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Mista Kazie Uko, wadda ya rabawa manema labarai a Umuahia, ranar Alhamis.

Ya kara da cewa, “bayan kaddamar da kwamitin binciken shari’a kan kwato kadarori da kudaden gwamnatin jihar Abia, gwamnan jihar, Dakta Alex Otti, OFR, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban ma’aikata nan take da dukkan Sakatarorin Dindindin a Ma’aikatan Gwamnatin Jihar.

Ya bayyana cewa magatakardan majalisar, Mista JohnPedro Iroakazi da kuma lauyan gwamnati Mrs. Uzoamaka Uche-Ikonne an cire su daga dakatarwar.

Sanarwar ta umarci wadanda aka dakatar da su mika aikin su ga manyan daraktoci a ma’aikatunsu.

Hakazalika sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya amince da nadin Misis Joy Maduka, darakta a ma’aikatar ilimi a matsayin shugabar ma’aikata ta riko.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *