Gwamna Zulum Ya Bada Biliyan Ɗaya ₦1B Ga Ƴan Kasuwar Da Gobara Ta Shafa A Barno

Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da bai wa ‘yan kasuwar da gobara ta ƙona musu shaguna, tallafin naira biliyan ɗaya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yaɗa labarai Isa Gusau ya fitar.

Sanarwar ta ce Gwamnan ya fitar da tallafin ne domin ragewa ‘yan kasuwar raɗaɗi da suke ciki bayan ƙonewar shagunansu da kuma irin wahalhalu da za su iya shiga idan ba su samu wani tallafi ba a nan gaba.

Za a kafa wani kwamiti don duba irin asarar da mutane suka yi da nufin taimaka musu da abin da ya kamata. In Ji shi.

Zulum ya kuma ce za a ɗauki matakai wajen ganin an kare afkuwar irin hakan a nan gaba saboda a baya an taɓa samun irin wannan gobara.

A karshe ya yi kira da a kwantar da hankula a yayin da gwamnati ke ƙoƙarin ganin an tallafa wa mutanen da abin ya shafa don rage musu raɗaɗi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *