Gwamnan Abba Yayi Allah Wadai Da Masu Safarar Kwayoyi A Jihar

FB IMG 1719671782992

Daga Abdu Ado K/Naisa

Zamu dauki mataki tare da saka kafar wando tsala don maganin masu irin wannan dabi’a

Alfijir labarai ta ruwaito a wata ziyarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai hukumar karota, ya yaba da irin kokarin da hukumar ke gudanarwa  bayan duba kayan aiki na manyan motoci da kuma irin kayayyakin da hukumar ta kama na kwayoyi da kayan maye.

Gwamnan yayi Allah Wadai da wadanda ya kira marasa kishin jihar Kano, wadanda suke taimakawa masu Harkar kwayoyi wajan tsaya musu don basu kariya.

Ya kara da cewar abin takaici ne hukuma ta kama kayan laifi! Amma wasu suyi kwance-kwance su karbi court order don dakile ayyukan gwmnati.

Abba Kabir yace zamu dauki mataki tare da saka kafar wando tsala don maganin masu irin wannan dabi’a

Gwamnan ya ja hankalin jami an hukumar da su kara jajircewa da yin aikinsu cikin tsari da doka domin magance bata gari a duk inda suke.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *