Gwamnan Jigawa Ya Nada Dr Yau Sara Shugaban (SEIMU) Da Mutane 10 A Wasu Hukumomi

Gwamna Malam Umar Namadi ya amince da nadin shugabannin hukumomi 11.

Alfijir Labarai ta rawaito Dr. Ya’u Ahmed Sara malami ne shi a Jami’ar Bayero dake jihar Kano a Tsangayar koyar da ilimin nazarin koyar da halayyar ɗan adam (Psychology), shine wanda aka naɗa darakta Janar na Sashin Kula da Sa ido na Jiha (SEIMU)

Ragowar aka nada sune:

1. Dr. Abbas Jafaru – Mafi kyawun Abbas Jafaru
Babban Sakatare, Kwamitin Kimiyya da Makarantun Fasaha

2. Alhaji Sale Zakar Kafin Hausa
Babban Sakatare, Hukumar Gyara

3. Dr. Mubarak Abdul Wahab Hassan
Babban Sakatare, Ofishin Ilimin Musulunci

4. Dr. Muhammad Hassan
Manajan Darakta, Galaxy ITT

5. Nasiru Sabo Idris
Shugaban Ma’aikatar Harajin Cikin Gida

6. Dr. Suleman Rufa’I Train
Darakta Janar na Cibiyar Binciken Noma ta Jigawa

7. Engr. Abbas Muhammad Lalai
Manajan Daraktan Hukumar Kula da Titin Jigawa (JIRMA)

8. Dr. Kassim Muhammad
Darakta Janar, Due Process and Project Monitoring Bureau

9. Dr. James Garba
Babban Sakatare, Ofishin Kididdiga

10. Hamza Maigari – The Best Of Hamza Maigari
Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Jigawa (JICHMA)

Sanarwar ta ce nadin wadanda aka nada domin yiwa jihar hidima a wannan matsayi ya dogara ne da cancanta, da kuma jarircewarsu wajen hidima ga Al’umma.

Hakki ne da ya rataya a wuyanku ku tabbatar wa al’ummar Jihar Jigawa cewa, lallai kun cancanci ku kara wa gwamnati himmar da za ta ciyar da rayuwar al’umma gaba daya,” inji SSG.

Ya kuma bukaci daukacin wadanda aka nada da su yi aiki tukuru don ganin an aiwatar da manufofin wannan gwamnati da tsare-tsare da ayyukanta.

Kamar yadda Ismaila Ibrahim Dutse
Jami’in Hulda da Jama’a
Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa ya wallafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM​

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *