Gwamnan Jihar Jigawa Ya Rantsar Da Kwamishinoni Tare Da Gargadinsu

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya gargadi sabin kwamishinonin da ya nada da cewa bazai yarda da dabi’ar lalaci a gwamnatinsa ba.

Gwamnan dai ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi Jim kadan bayan rantsar da kwamishinonin a gidan gwamnatin jihar dake Dutse da yammacin ranar Laraba.

Kazalika ya taya su murnar samun kansu cikin kunshin jami’an gwamnatinsa harma yaja hankalin su wajen yin aiki tukuru ta hanyar sanya idanu da bibiyar ayyukan ma’aikatun da aka turasu bawai zaman office ba.

Da yake jawabin godiya ga gwamnan amadadin sauran Kwamishinonin sabon kwamishinan yada labarai matasa da wasanni Alhaji Sagiru Musa yayi alkawarin yiwa gwamnatin biyayya da aiwatar da ayyukan ciyar da jihar Jigawa gaba kamar yadda ke kunshe cikin manufofin gwamnan 12.

Kwamishinonin dai sun hada da Dakta Isah Yusuf Chamo kwamishinan ma’aikatar Ilimi a manyan makarantu sai Dakta Lawan Yunusa Danzomo kwamishinan ilimi a matakin farko da Farfesa Hannatu Sabo ma’aikatar kudi da kuma Hajiya Hadiza T Abdulwahab kwamishinar mata da walwala sai Hon Ibrahim Garba Hannin-Giwa ma’aikatar Ruwa da Babban Gida Umar Gantsa kasafi da tsare-tsare sai kuma Engineer Gambo Barau ma’aikatar Ayyuka da sifiri.

Sauran sune Hon Muttaka Namadi Ringim ma’aikatar Gona da Dakta Muhammad Abdullahi Kainuwa maaikatar lafiya da Muhd Garba MK ma’aikatar kananan hukumomi da kuma Muhammad Alhassan ma’aikatar kasa da kuma Sagiru Musa ma’aikatar yada labarai sai Dakta Musa Adamu Aliyu ma’aikatar shari’a da kuma Auwalu Dalladi Sankara ma’aikatar ayyuka na musamman.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *