Alfijir Labarai ta rawaito mai girma
Gwamnan Jihar Kano, ya amince da mayar da Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, PCACC, domin kammala wa’adinsa.
Ku tuna cewa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barr Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.
Wannan matakin gwamnatin ta dauka tayi ne cikin bin umarnin kotu da ta bayar.
Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna ya wallafa.
Allah yayi riko da hannunsa yafiddashi Kunyar Abba da Jamaar Kano
Hakan yayi Allah yatabbatar da dugadugansa yabashi ikon adalci
Allah karawa jaridar Alfijir mutunci da albarka da farinjini