Gwamnan Kano Ya Naɗa Sabon Ciyaman Ɗin Kungiyar Kwallon kafa Ta Kano Pillars

Alfijr

Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya maye gurbin Ciyaman ɗin Kungiyar Ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Surajo Shuaibu Yahaya, da shugaban hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima a yau Laraba

Idan kun tuna ranar Asabar ne hukumar shirya gasar firimiya ta Ƙasa, LMC ta kori tsohon Ciyaman ɗin na Kano Pillars, Suraj Yahaya, daga ƙungiyar.

Alfijr

Korar Ciyaman ɗin ta biyo bayan laifin cin zarafin mataimakin alƙalin wasa da awa ka ganshi a wani faifan bidiyo yana yawo a kafafan sada zumunta.

A wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa,

Wata sanarwa da sakataren yaɗa Labaran gwamnan ya fitar Abba Anwar yace, Ganduje ya ce “Kamar yadda kungiyar Kano Pillars ke kara fuskantar matsin lamba a gasar firimiya ta kasa, zai yi kyau a samu shugabancin da zai jagoranci ƙungiyar cikin da a.

Alfijr

Gwamnan ya ce Ibrahim Galadima, shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, yanzu zai maye gurbin Ciyaman ɗin Kano Pillars FC na yanzu, Surajo Shu’aibu Yahaya, a matsayin muƙaddashi, kafin a naɗa Ciyaman na dindindin.

Kuma nadin yaq fara aikinan take, inji shi

Slide Up
x