Gwamnan Jihar Lagos Ya Raba Sabbin Motoci 13 Ga Gwarazan Malamai

Alfijr

Alfijr ta rawaito Gwamna jahar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya danƙa mukullan sabbin motoci fil guda 13, ƙirar SUV ga gwarazan malamai da aka zaɓo a shiyyoyin ilimi shida na jihar.

Malaman sun samu nasarar samun sabbin motocin saboda ƙwazon su da kuma ƙware wa wajen amfani da dabarun zamani wajen koyar da ɗalibai.

Alfijr

Waɗanda su ka samu motocin na daga cikin waɗanda aka zaɓo domin bada lambar yabo ta malamai ta shekarar 2021, wanda kwamitin tantancewa, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar malamai masu zaman kansu a Nkjeriya, Lai Koiki.

A wajen bikin karramawar ta malamai ta 2021, wanda aka gudanar a gidan Ikeja, Sanwo-Olu ya bayyana cewa shirin ya yi daidai da ƙudurin yin amfani da ilimi a matsayin wani makami na sauya duniya da kuma tasiri a harkar koyarwa.

Alfijr

Sanwo ya ce wannan tukwicin da aka samu shi ne na sadaukar da kai, da jajircewa a tsakanin malaman na jihar.

A cewarsa, hanya ce mai kyau ta zaburarwa da karfafa gwiwar hazikan malamai, a fagen neman ilimi mai inganci da inganci ga daliban da ake so.

Alfijr
Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa

Slide Up
x