Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin Hisham Habib shugaban kungiyar ƴan jaridu ta yanar gizo reshen jihar Kano a matsayin Manajan Daraktan gidan rediyon Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito Naɗin wanda ya fara aiki nan take a wata sanarwa da Hisham ɗin ya fitar, wanda kuma ke rike da muƙamin muƙaddashin mai magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hisham Habib gogaggen ɗan jarida ne, ya yi digirinsa na farko a fannin turanci a jami’ar Bayero Kano, sannan ya yi digiri na biyu a fannin koyon aikin jarida.
Kafin wannan naɗin, Hisham ya yi aiki a matsayin ma’aikaci a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano kuma ya riƙe muƙamin jami’in hulɗa da jama’a a ma’aikatar shari’a.
Har ila yau, ya yi aiki a matsayin mai ba da rahoto a fitattun kafafen yaɗa labarai da suka haɗa da jaridar Daily Trust da Daily Independent.
Bugu da kari, ya yi aiki a matsayin shugaban Media Cave Limited, wata kafar yada labarai mai zaman kanta kuma mawallafi a jaridar News Tunnel.
Hisham yanzu haka shine shugaban yan jaridun yanar gizo wato Kano Online journalist.
Kungiyar ta yan jaridar yanar gizo suna taya shugabansu murnar wannan mukami, Allah yasa ya zamarwa al’ummar Kano alheri baki daya ameen.
Ana sa ran naɗin Hisham zai ƙara inganta ayyukan gidan rediyon Kano da kuma ƙara azama wajen isar da aiki mai inganci ga al’ummar jihar Kano da da maƙwambtan jihohi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ