Gwamnan jihar Kano ya sanya hannu kan dokokin kirkirar sabbin ma’aikatu gwamnatin jihar har guda hudu.
Gwannan ya ce kirkirar sabbin ma’aikatun zai kara taimakawa wajen inganta cigaban jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu.
Sanarwa ta ce sabbin ma’aikatun da aka sanyawa dokokinsu hannu su ne kamar haka:
1. Kano State Protection Agency (KASPA)
2. Kano State Signage and
Advertisement Agency (KASIAA)
3. Kano State Information and Communication Technologies Development Agency (KASITDA)
4. Kano State Small and Medium Enterprises Development Agency (KASMEDA)
Wadannan ma’aikatun shiga cikin kunshin wadanda jihar Kano ta ke da su, wadanda ake da yakinin za su taimaka matuka wajen inganta masana’antu da kula da tallace-tallace da kuma kare mutane da dai sauransu.
Gwamna Yusuf ya ce sanya hannu kan dokokin wata gagarumar nasara ce ga gwamnatinsa a kokarinta na samar da cigaba mai dorewa a jihar Kano.
Ya ce sabbin ma’aikatun za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da aikin yi ga matasa da jawo hankalin masu zuba hannun jari da dai sauransu.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD