Gwamnan Kano yayi zazzafan gargadi da jan kunne ga Kwamishinoninsa da manyan jami’an gwamnati

IMG 151140 22925 1758550322304

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa duk wani kwamishina da ke kokwanto ko kuma ke ƙoƙarin cin dunduniyar gwamnati saboda komawarta Jam’iyyar APC, ya kamata ya shirya ajiye aikinsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake jagorantar zaman Majalisar Zartarwar Jihar karo na 38 da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Kano.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani jami’i da ke aiki a ƙarƙashin gwamnati amma a lokaci guda yana aiki da wata jam’iyya ta daban ba, yana mai cewa hakan na iya kawo tangarda ga tafiyar gwamnati.

Yusuf ya ƙara da cewa duk wani kwamishina ko babban jami’i da ke da niyyar sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya, ya dace ya ajiye aikinsa domin baiwa gwamnati damar naɗa wanda zai yi aiki da cikakkeyar biyayya.

Gwamna Yusuf ya kuma buƙaci ‘yan majalisar zartarwar jihar da su ci gaba da ba da gudunmawarsu domin tabbatar da nasarar manufofin gwamnatin Jam’iyyar APC da kuma ci gaban al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *