Gwamnan Katsina Ya Umarci A Binciki Malamin Da Yayi Lalata Da ɗalibarsa A Dandume

FB IMG 1702067553881

Gwamna Raɗɗa ya umarci a binciki Malamin da yayi lalata da ɗalibarsa a Dandume

Alfijir labarai ta rawaito gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin yin bincike game da malamin makarantar sakandire da ake zargin yayi lalata da ɗalibar sa a ƙaramar hukumar Dandume dake jihar Katsina.

Hakan na ƙunshe ne Cikin wata sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai dake ofishin sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Aliyu Yar’adua, a ranar Juma’a ya sanyawa hannu a madadin fadar gwamnatin jihar.

Sanarwar tace, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya samu rahoto da ake zargin wani malamin makarantar sakandare mai suna Lawal Ibrahim, da ake zargin yayi lalata da wata ɗalibarsa.

Da jin hakan ba da jimawa ba, gwamnan jihar ya umurci kwamishinar ma’aikatar ilmin firamare da na sakandare ta jihar Katsina da su gaggauta dakatar da malamin mai suna Lawal Ibrahim, sannan a gudanar da bincike a kan lamarin inji sanarwar.

Kazalika, gwamnan ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina da ya binciki lamarin, tare da bincikar baturen ‘yan sandan (DPO) na ƙaramar hukumar Dandume wanda ake zargi da karɓar na goro domin lalata maganar game da batun malamin makarantar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *