Gwamnati Zata Rushe Wani Ofishin Ƴan Sanda Da Sauran Wasu Gine-Gine

Shehu Ahmed, babban sakataren hukumar raya babban birnin tarayyar Nijeriya (FCDA), ya ce gwamnatin tarayya (FCTA) za ta rusa dukkan gine-ginen da ke hanyoyin ruwa a fadin babban birnin kasar.

Alfijir Labarai ta rawaito Ahmed, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya ce, wasu gine-gine na hana ruwa gudu ta hanyayoyinsa, wanda ke haddasa ambaliya da aka samu a wasu sassan birnin.

A makon da ya gabata ne Hukumar FCTA ta ayyana yankin Trademore da ke unguwar Lugbe a Abuja a matsayin wani bala’i sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankin a ranar 23 ga watan Yuni.

Ba za mu zuba ido mu na ganin wannan matsalar na cutar da mutume ba, da kuma saba tsarin Abuja ba,” in ji Ahmed.

Da yake karin haske, Ahmed ya ce: “An yiwa gine-ginen da ke cikin Estate Trademore lamba domin rushewa.

An yi gargadin shekarun baya amma mazauna wannan wajen sun ci gaba da yin kasada da rayukansu da na wasu.

“Ta hanyar ayyana Trademore a matsayin yankin bala’i, mun gaya wa mazauna wurin su yi ƙaura, saboda ambaliyar ruwa na iya zuwa a kowane lokaci, sun san wannan kuma sun sha fama da shi tsawon shekaru. “

Ahmad, wanda kuma shi ne shugaban tawagar ministoci na musamman kan dakile ambaliyar ruwa, ya ce za a rushe ofishin ‘yan sanda tare da wasu gine-gine.

Mun shigar da rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja kuma mun samar da wurin da ya dace domin gudanar da ayyukansu da kuma yaki da miyagun laifuka,” In ji shi.

Sakataren zartarwa ya kuma ce yankin ba shi da tsarin ginin da FCDA ta amince da shi kuma yankin da aka yi ambaliya akai-akai zai iya zama mafi kyau a bar shi a matsayin wuraren kore ba wurin zama ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *