Gwamnatin Kano Da Hukumar NEMA Sunyi Rabon Kayan Agaji Ga Al’ummar Jihar

Hukumar dake kula da bada agajin gaggawa ta Kasa (Nema) da hadin guiwar Gwamnatin Kano sun jagoranci rabon tallafi ga mutanen iftila’in ambaliyar ruwa ta afkawa.

Alfijir Labarai ta rawaito an yi rabon ne a Maganda Road in da aka kaddamar da rabon tallafin da suka kunshi kayan Abincin da takin Zamani da Katifu da Injunan Markade da kekunan dinki da Risho tare da Barguna hadi da tabarmi da bokitai da kuma gidan sauro da sauran kayayyakin more rayuwa. .

Mataimakin Gwamnan Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya wakilici Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf a wurin taro, tare da rakiyar Sakataren Gwamnatin jihar Kano Dr Abdullahi Baffa Bich da sauran jami’an Hukumar ta NEMA.

📸 Radio Kano

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Slide Up
x

One Reply to “Gwamnatin Kano Da Hukumar NEMA Sunyi Rabon Kayan Agaji Ga Al’ummar Jihar”

  1. Allah Ya Sakawa Gwamnatin kano Da Alkhari Allah yaqara Data Darajar mu bakidaya Mutanan 🅰MANA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *