Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar dawowar makarantu na firamare da na sakandare domin cigaba da Karatu a sabon zangon na shekarar 2025/2026.
Wata sanarwa da daraktan wayar da kai na ma’aikatar Ilimi,ta Kano Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ta bayyana cewa, daliban makarantu na kwana za su koma a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, yayin da daliban makarantu na rana za su koma a Litinin, 8 ga Satumba, 2025.
An shawarci iyaye da masu kula da yara su kula da wannan jadawalin domin tabbatar da cikakken bin doka, inda aka gargadi dalibai da suka saba dokar cewa za su fuskanci hukunci.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya yi fatan alheri ga malamai da ɗalibai wajen sabon zangon karatu mai zuwa..
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t