Gwamnatin Kano Ta Bada Sabon Umarni Kan Dokar Hana Achaba.

best seller i

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa dokar hana daukar fasinja ta shafi masu sana’ar achaba ne kawai, ba ta shafi masu amfani da LIFAN domin goyo ko jigilar kaya ba. Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Kwamishinan Shari’a na Kano yayin wata ganawar aiki da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bakori.

A cewar Kwamishinan Shari’ar, gwamnatin Kano na ƙoƙarin kawar da dukkan barazanar matsalar tsaro da ta fara kunno kai sakamakon wayar gari da masu sanaar achaba a cikin birni. Ya ce an dauki wannan mataki ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman ma ganin yadda wasu ke amfani da babur wajen aikata laifuka ko haifar da cinkoso a manyan hanyoyi.

Sai dai Kwamishinan ya jaddada cewa masu goyo (LIFAN) ba su cikin waɗanda aka haramta musu zirga-zirga, matuƙar suna bin ƙa’idodi, kamar amfani da takardu na doka da kiyaye ka’idojin tuki.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Bakori ya yi alkawarin tabbatar da yadda jami’ansa za su aiwatar da umarnin bisa gaskiya da adalci. Ya ce rundunar za ta ci gaba da wayar da kai domin tabbatar duk wanda aka kama da mashina achaba ya karya doka kuma za a hukunta shi, yayin da masu LIFAN kuma za a bar su su ci gaba da harkokinsu ba tare da tsangwama ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *