Gwamnatin Kano Ta Dage Ranar Komawa Makarantu a Jihar

FB IMG 1719671782992

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnatin jihar Kano ta dage ranar da za a koma makarantun firamare da na sakandire domin fara karatun shekarar 2024/2025.

Alfijir labaria ta rawaito wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu ta ruwaito kwamishinan ilimi Alhaji Umar Haruna Doguwa yana bayyana cewa an yanke shawarar dage ranar da za a koma makarantar ne saboda wasu dalilai na gaba gaggawa.

Umar Doguwa ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba ma’aikatar ilimi ta jihar kano za ta sanar da wata rana da za a komawa makarantun.

“Ina so in sanar da dalibai da iyayensu cewa sanarwar da aka bayar tun farko na komawa makarantu a ranakun 8 da 9 ga Satumba, 2024, yanzu an dage ta, saboda wasu dalilai na gaggawa da za su taimaka wajen inganta yanayin koyo da koyar da yaranmu. za a sanar da wata ranar nan gaba kadan, “in ji kwamishinan.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *