Gwamnatin Kano Ta Hukunta Wani Perm Secretary Kan Zargin Badaƙala

Gwamnatin jihar Kano ta amince da gaggauta sauya babban sakatare na hukumar kula da ma’aikata, Mustapha Safiyanu Kabuga bisa zargin bugawa da sanya hannu kan takardun nadin mukamai a ma’aikatan jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakataren gwamnatin jiha Kabiru Sa’idu Magami a madadin sakataren gwamnatin jiha SSG, Dr. Baffa Bichi. .

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya fitar a ranar Asabar, ta ce, gwamnati ta kafa kwamitin tantancewa na mutane uku a karkashin jagorancin mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin ma’aikata, Dakta Sulaiman Wali. Sani ya binciki lamarin sannan ya mika rahotonsa cikin kwanaki goma.

Sanarwar ta ce, ”An sake mayar da famanan sakataren zuwa ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati har sai an kammala aikin kwamitin.

“Hakazalika, an nada Salahuddern Isa Habib a matsayin babban sakataren dindindin na hukumar daga ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, 2023.”

‘’Kwamitin yana da hurumin tantancewa da raba takardun karin mukamai na ma’aikatan jihar, wadanda wasu ma’aikatan hukumomi suka rubuta; da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga gwamnati bisa ka’idojin da suka dace.’’ in ji sanarwar.

Solacebase

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *