Gwamnatin Kano ta sanar da ranar fara hutu ga Makarantun Firamare da Sakandare a fadin jihar

FB IMG 1764772548155

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu a matsayin ranar fara hutun Azumin Ramadan da Sallah ga dukkanin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.

A wata sanarwa da Daraktan wayar da Kai na ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano Musbahu Sani Yakasai ya fitar, ya ce daliban firamare da sakandire za su fara hutun ne daga Lahadi 1 ga Maris, 2026 kamar yadda jadadalin karatun bana ya nuna.

Sanarwar ta bukaci iyaye da su je daukar ‘ya’yansu tun da safiyar ranarJuma’a 27 ga Fabrairu, 2026 domin fara hutun.

Sanarwar ta kara da cewa daliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, yayin da daliban makarantun jeka ka dawo za su koma ranar Litinin 23 ga Maris, 2026.

An kuma bayyana cewa zangon karatu na biyu zai ci gaba daga ranar 22 ga Maris, 2026, kuma zai kare a ranar Asabar 18 ga Afrilu, 2026.

Gwamnatin jihar ta umarci dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su bi wannan umarni ba tare da saba wa ka’ida ba, tana mai gargadin cewa duk makarantar da ta karya wannan doka za a dauki matakin ladabtarwa a kanta.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya bukaci iyaye da su tabbatar yayansu sun koma makarantunsu a ranar da aka tsara hakan.

Ya kuma gode wa iyaye da al’ummar jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa Ma’aikatar Ilimi, tare da yi wa dalibai fatan kammala Azumin Ramadan cikin nasara da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *