Gwamnatin Kano Ta Yi Martani Kan Ɗaga Tuta A Fadar Sarki Ta Nassarawa

FB IMG 1717887280031

Gwamnatin Kano ta yi watsi da batun ɗaga tutar masarauta da aka yi a gidan sarki na Nassarawa, wurin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune a ciki.

Alfijir labarai ta ruwaito mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya yi fatali da batun ɗaga tuta a Fadar Nassarawar, inda ya ce hakan wani yunƙuri ne na jan hankalin al’umma.

Ya shaida wa manema labarai cewar, “hakan wani yunƙuri ne na jan hankalin al’umma amma babu shakku ko tantamar cewar Sanusi ne Sarkin Kano.”

Tutar, wata alama ce ta iko dake nuni da cewar Sarki na nan, a kullum ana ɗaga ta da misalin karfi 6 na safe a kuma sauketa da 6 na yamma.

Duk lokacin da sarki ba ya cikin fada ko ya yi balaguro tutar za ta kasance a sauke.

Idan zaku tuna a ranar Alhamis ce aka ɗaga tutar da misalin karfe 6 na safiya a Fadar Nassarawa, abin da ya haifar da kace-nace da ma raɗe-raɗi.

Kowanne daga cikin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II na ikirarin shi ne Sarkin Kano kuma suna ci gaba da aiwatar da ayyukan sarauta.

An ɗaga irin wannan tuta a Fadar Gidan Rumfa, inda Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ke zaune.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *