Gwamnatin Najeriya Ta Gurfanar Da Shugaban Meyetti Allah Kautal Hore Gaban Kuliya

FB IMG 1710374877650 edit 3191910382845

Gwamnatin Najeriya ta Gurfanar da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo da ake tsare da shi a gaban kotu bisa zargin ta’addanci.

Alfijir labarai ta rawaito cikin tuhume-tuhumen da aka gabatar a ranar 12 ga watan Maris, ana zargin Bodejo da zagon kasa ga tsaron kasa ta Najeriya ta hanyar kafa kungiyar yan banga da ba da makamai ba tare da izini ba.

An kama Bello Bodejo ne a Ranar 23 ga watan Janairu a ofishin Miyetti Allah da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar da ƙara a Ranar 5 ga watan Fabrairu yana neman a cigaba da tsare Bodejo har sai lokacin da DIA ta kammala binciken da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

Mai shari’a Inyang Edem Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja, bisa karar da aka shigar, ya bayar da umarnin a tsare Bodejo na tsawon kwanaki 15.

A lokacin da wa’adin kwanaki 15 ya kare a ranar 22 ga watan Fabrairu, alkalin kotun ya baiwa Gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki bakwai ta shigar da karar Bodejo.

Sai dai a zaman da aka yi a Ranar Laraba, hukumar leken asiri ta Defence (DIA) da ke Abuja taki gabatar da Shugaban Miyetti Allah dake tsare a gaban babbar kotun.

Mai shari’a Ekwo, bayan da ya amsa hujjoji daga lauyoyin, ya sanya ranar 22 ga watan Maris domin yanke hukunci kan ko a amince da bukatar belin ko a’a.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *