Gwamnatin Najeriya Ta Mika Cibiyar Samar Da Lantarki Ta Zungeru Ga Yan Kasuwa

FB IMG 1708512818674

Gwamnatin Najeriya ta miƙa ragamar harkokin cibiyar wutar lantarki na Zungeru zuwa ga wani kamfani mai zaman kansa na Penstock Limited.

Alfijir labarai ta rawaito an bayyana haka ne a taron farko na hukumar NCP da ke tantance kadarorin gwamnati da suka kamata a sayar a bana da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Ana sa rai matakin zai inganta harkar samar da wutar lantarki tare da bayar da gudummawa sosai ga biyan buƙatun ƴan ƙasa game da makamashi.

An cimma yarjejeniyar ranar 13 ga watan Disamban 2023 tsakanin hukumar kula da kadarorin gwamnati BPE da kamfanin na Penstock Limited.

Bayan amincewar hukumar NCP, kamfanin ya amince ya biya kashi hamsin cikin 100 na kuɗin soma aiki ranar 5 ga watan Janairu.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima wanda ya jagoranci taron ya bayyana ƙudurin gwamnatin tarayya na sake fasalta bankin tallafawa ayyukan noma domin haɓaka ɓangaren noma da samar da abinci a ƙasa.

Da yake magana a taron, Shettima ya bayyana irin rawar da bankin zai taka wajen samar da abinci a ƙasa inda ya yi magana kan rassan bankin da ke yankunan Najeriya.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *