Gwamnatin Najeriya Ta Yiwa Yan Kwadago Tayin N62,000 A Mafi Karancin Albashi

IMG 20240608 WA0000

Gwamnatin Najeriya ta yi wa ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar tayin ba su naira 62,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi a ƙasar.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon sa’o’i ɓangarorin biyu suna tattaunawa kan mafi ƙanƙantar albashin.

A nata ɓangare ƙungiyar ƙwadagon ta rage buri zuwa naira 250,000, saɓanin naira 494,000 da a baya ta buƙaci gwamnatin ta bayar

A farkon makon nan ne gwamnatin ƙasar ta buƙaci ƙungiyar ƙwadagon ta janye yajin aikin da ta fara, bayan da gwamnatin ta alƙawarta yin ƙari kan naira 60,000 da ta yi a makon da ya gabata.

Kawo yanzu dai ɓangarorin biyu sun tashi zaman ba tare da cimma matsaya ba, sai dai sun alƙawarta ci gaba da tattaunawar domin samun daidaito.

To sai dai ba a sani ba ko wannan motsi da duka ɓangarorin biyu suka yi ka iya sanyawa a cimma matsaya, don kauce wa komawa yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon za su yi, da zai iya durƙusar da harkokin tattalin arzikin ƙasar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *