Gwamnatin Najeriya Ta Ƙara Ranakun Hutun Karamar Sallah

FB IMG 1710375660100

Gwamnatin tarayya ta amince da ranar Alhamis, 11 ga Afrilu, 2024, a matsayin kari a kan ranakun hutun sallar Eid-El-Fitr ta bana.

Alfijir labarai ta rawaito wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dr Aishetu Gogo Ndayako, babban sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida da ya ba da izini a safiyar yau Talata.

Sanarwar ta rawaito Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya nanata kudurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da zaman lafiya da wadata a Najeriya domin kowa ya samu ci gaba.

“Mai girma ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, yayin da yake taya al’ummar musulmi murnar kammala wata guda na ibada, ya nanata kudurin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) na samar da kasar Najeriya lafiyaiya da wadata ga kowa da kowa ya samu ci gaba. ,” in ji sanarwar.

Tun da fari dai, gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024, a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Sallah.

Sai dai kuma rashin ganin jinjirin wata a jiya Litinin, lamarin da ya sa aka ayyana ranar Laraba a matsayin Eid-el-Fitr.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *