Gwamnatin Nigeriya ta Dauki Matakan Rage Tsadar Iskar Gas A Kasar

FB IMG 1708616850937

Gwamnatin tarayya ta haramta fitar da iskar gas din da ake amfani da shi wajen girki, a wani yunkuri na magance karancinsa a cikin gida da kuma karyar da farashin sa.

A ranar Alhamis din nan aka fadawa dilolin Gas (LPG) a Najeriya da masu ruwa da tsaki a masana’antar da su daina fitar da Gas din daga Najeriya domin wadata al’ummar kasar da shi da kuma karyar da farashin sa .

Bincike ya nuna cewa farashin man iskar gas mai nauyin kilogiram 12.5 a Abuja, Legas, Kano da wasu jihohi ya haura kusan Naira 18,000. Gas din da aka siyar da shi kasa da N9,000 a watan Nuwambar bara.

Dillalan LPG karkashin kungiyar masu sayar da iskar gas ta Najeriya sun yi hasashen a tsakiyar shekarar da ta gabata cewa silinda mai nauyin kilogiram 12.5 zai kai Naira 18,000 sakamakon hauhawar farashinsa.

Amma har ya zuwa yau (Alhamis), farashin Gas din ya ci gaba da tashi a arewa, sai dai yawan masu amfani da shi a hankali suna komawa ga yin amfani da gawayi.

Sai dai da yake magana a wajen taron bitar masu ruwa da tsaki na cikin gida da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, Ekpo ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta bukaci masu samar da iskar gas din da su daina fitar da shi zuwa kasashen waje.

Ya bayyana sunayen wasu kamfanonin mai na kasa da kasa da suka hada da Mobil, Shell, da Chevron a matsayin masu samar da man, yana mai jaddada cewa gwamnati na yin cudanya da su wajen yin saukar da farashin iskar gas.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *