Gwamnatin Zamfara Zata Fara Aikin Hanyoyin Cikin Garin Gusau

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin, Dauda Lawan ta sanya hannu kan wata yarjejeniya na fara aikin hanyoyin cikin gari kashi na daya dake babban birnin jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito Kashi na daya na aikin shine hanyar da ta ta shi daga gidan gwamnati zuwa titin Bello Bara’u da titin Tankin Ruwa, da hanyar tsohuwar kasuwa, da shataletalen da ke kusa da ofishin ‘yan sanda da dai sauransu.

Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar ne a zauren majalisar na gidan gwamnati.

Ya kara da cewa, samar da ababen more rayuwa wani bangare ne na kudirin Gwamnatin Jiha na sabunta birnin, da nufin samar da yanayi mai kyau kasuwanci ya bunkasa don samun saukin rayuwa.

Sanarwar ta kara da cewa “Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani katafaren kamfanin gine-gine, Ronchess Nigeria Limited domin fara shirin sabunta birane a jihar.

“Gwamna Lawal ya nanata kudirin Gwamnatin sa na ganin an dawo da rugujewar ababen more rayuwa ta hanyar sake gina sabbi da kuma gyara tsofaffin da suka fara daga Babban Birnin Jiha.

“Rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar yana nuna cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara wani aiki da zai sauya yanayin Jihar.

“Gwamnati za ta samu nasarori da dama tare da hadin kan mutanen kirki na jihar Zamfara, Sabunta birni yana ɗaya daga cikin dabarun da aka yi amfani da su don aiwatar da aikin ceto jihar.”

Da yake mayar da martani a madadin kamfanin gine-ginen, babban daraktan kamfanin na Ronchess, Samson David ya bayyana cewa suna son su maida jihar Zamfara tamkar jihar kaduna, ya kuma yabawa gwamnatin jihar Zamfara da ta zabesu taga sun cancanci a basu kwangilar tare da bada tabbacin za su gudanar da aiyukan cikin nasara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *